An sa dokar hana Musulmin Rohingya haihuwar 'ya'ya sama da biyu

Hukumomi a kasar Burma sun kara jaddada haramcin da suka dade da sa wa , wanda ya hana Musulmai 'yan kabilar Rohingya haihuwar 'ya'ya sama da biyu.

Jami'an gwamnati wadanda suka yi imanin cewa yawan hayayyafar 'ya'ya da 'yan kabilar Rohingya ke yi na daga cikin abubuwan dake janyo rikicin addini tsakaninsu da mabiya addinin Buddha, zasu sa a yi aiki da haramcin ne a wasu sassa na jihar Rakhine .

Daruruwan mutane ne aka kashe, dubban suka yi gudun hijira sakamakon rikicin addinin da ya barke a jihar bara.

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch ta bayyana haramcin da aka sa, na takaita haihuwar 'ya'ya biyu, da cewa abin kyama ne, kuma rashin imani ne.

Kasar Burma dai na yi wa Musulmi 'yan kabilar ta Rohingya kallon bakin haure, ta kuma hana masu izinin zama 'yan kasa.