Za a sake fasalin matakan sa ido a Birtaniya

Praministan Birtaniya, David Cameron
Image caption Praministan Birtaniya, David Cameron

Praministan Birtaniya, David Cameron zai kafa wani kwamiti na aiki da cikawa wanda zai sake nazarin salon da gwamnati ke amfani da shi wajen tunkarar matsalar ta'addanci, da cusa akidar tsattsauran ra'ayi a zukatan matasa Musulmi.

Kwamitin zai hada da manyan ministocin gwamnati da jami'an tsaro.

Kkuma zai mayar da hankali ne kan matakai na zahiri, ciki har da matakan da za a iya dauka kan malaman addini masu kaifin ra'ayi.

Sheikh AbdurRazak Ibrahim na majalisar Fatwa a Turai ya ce akwai bukatar sa ido kan wasu malamai masu wa'azi.

Matakin ya biyo bayan kashe wani sojan Birtaniya ne a London da wasu matasa su biyu suka daddatsa suna kuma yin takbir.

A shekara ta 2011 ne gwamnatin ta rage yawan kudaden da aka ware ma wani shiri na yaki da cusa tsauraran ra'ayoyi.