An kai harin rokoki a unguwannin Hezbollah

Wasu makaman roka biyu sun fada a wata anguwa ta Beirut, babban birnin kasar Lebanon, wadda ke karkashin ikon kungiyar Hezbullah.

An raunata mutane hudu.

Rahotanni na cewa ma'aikata ne yan kasar Syria.

An kai harin ne kwana guda bayan wani jawabi da jagoran Hezbullah, Hassan Nasrallah ya yi inda a ciki yake cewa dakarunsa zasu ci gaba da fada a bangaren shugaba Assad a yakin basasar kasar Syria.

Tuni majalisar koli ta 'yan adawar Syriyar ta yi allawadai da wannan ikirarin na Nasrullah.

Kuma kwamandojin 'yan tawayen Syria sun lashi takobin daukar fansa a Labanon.