Yunkurin kawo karshen rikicin Syria

Ministan harkokin wajen Syria, Walid Muallem ya ce gwamnatinsu ta amsa a baka cewa zata halarci taron sulhun da za a yi a Geneva.

Lokacin da yake magana yayin wata ziyara a Bagadaza, Walid Muallem ya ce taron na Geneva wata babbar dama ce ta samun warware rikicin kasar a siyasance.

Wannan ne karon farko da gwamnatin Syria ta fito fili ta ce zasu halarci taron wanda Amurka da Rasha suka bada shawarar gudanarwa.

Babbar kungiyar 'yan adawan Syrian na ci gaba da gudanar da taro a birnin Santambul yanzu haka da nufin tsara yada zasu tunkari taron sulhun.

Amma dai ita Majalisar 'yan adawar Syriar ta ce zata halarci taron ne kawai idan shugaba Assad ya sauka, ya koma gefe guda.