Amaechi ya ce ba gudu ba ja da baya

PDP
Image caption Masu sharhi na ganin rikicin zai iya yin illa ga jam'iyyar

Gwamnan jihar Rivers a Najeriya kuma shugaban kungiyar gwamnonin kasar Rotimi Amechi, ya ce ba gudu ba ja da baya a takaddamar da ke tsakaninsa da uwar jam'iyyarsa ta PDP.

Yana magana ne kan nasarar da ya samu na sake lashe zaben kungiyar gwamnonin da aka yi a ranar Juma'a, da kuma badakalar da ta biyo bayan zaben.

Inda bangaren gwamna Jonah Jang na jihar Plateau wanda ya sha kayi, ya kafa na sa shugabancin.

Sannan kuma a ranar Litinin jam'iyyar PDP ta kasa, ta dakatar da Rotimi Amaechin bayan da ta ce ya aikata laifukan da suka sabawa tsarin mulkinta, ta hanyar rushe shugabancin karamar Hukumar Obiokpor.

Sai dai Gwamna Ameachi ya musanta wannan zargi:

"Wajibi ne jam'iyyata ta tashi tsaye domin kaucewa bita da kulli, gwamna bai rushe shugabancin karamar hukumar Obiokpor ba, ina fata kun fahimta.

Ina da ikon rushe su, zan iya rushe su yau din nan, na mika matakin ga majalisar dokoki, amma har yanzu ban yi hakan ba tukunna", a cewar Amaechi.

Fatan addu'a

Ana dai zargin bangaren shugaban kasa da hannu a cikin lamarin na, sai dai ya musanta hakan.

Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin siyasa Barrister Ahmed Gulak, ya ce shugaba Jonathan ba shi da hannu ko kadan a rikicin kungiyar gwamnonin da kuma halin da Amaechi ya samu kansa a jam'iyyar.

Gwamna Amaechi ya ce lamarin ba mai karewa ba ne anan kusa, sannan ya nemi magoya bayansa da su yi masa addu'a.

"Ban sani ba cewa ko a matsayi na na gwamna kuma dan jam'iyyar PDP, idan na nemi hakkina a jami'iyyar PDP to shi kenan hakan ya zama yaki da jam'iyyar ko yi mata zagon kasa?

Tunda suka yi amfani da dukkan damar da suke da ita a gwamnatin taerayyar, suka yake ni, amma duk da haka na ci zabe, me ya kamata su yi, sai su bi ni su godewa Allah domin wannan na nufin Allah ya nuna ikonsa", kamar yadda ya ce.

Karin bayani