ICC na nunawa Afurka banbanci, in ji AU

Tarayyar Afrika
Image caption An dade ana sukar lamarin kotun ta duniya a Afrika

Shugabannin kasashen Afrika da suka kammala taron kolinsu a Addis Ababa, baban birnin Habasha sun zargi kotun shari'ar laifukkan yaki ta duniya, da nuna bambancin launin fata ga nahiyar Afrika.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar bayan taron da aka fitar bayan bikin cika shekaru hamsin da kafa kungiyar.

Taron shugabannin ya kuma yanke shawarar kafa wata rundunar soja ta kai dauki cikin gaggawa.

Manufar ta ita ce tunkarar duk wata matsalar tsaro da ka iya tasowa, domin rage dogaro kan neman taimakon soji da na kudi daga wasu kasashe da ba na nahiyar ba.