Tarayyar Afirka ta zargi Kotun Duniya

Firayim Ministan Habasha Hailemariam Desalegn
Image caption Firayim Minista Hailemariam Desalegn ya zargi Kotun Duniya da yi wa 'yan Afirka bi-ta-da-kulli

Kungiyar Tarayyar Afirka ta zargi Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka da kafa wa 'yan Afirka "kahon-zuka" saboda launin fatarsu.

A cewar Firayim Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn, kungiyar ta Tarayyar Afirka dai tana adawa da yunkurin Kotun ta Duniya na yi wa Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya shari'a bisa tuhumce-tuhumcen cin zarafin bil-Adama.

Ya kuma kara da cewa kungiyar za ta kai batun gaban Majalisar Dinkin Duniya.

A watan Yuli ne dai ake sa ran fara shari'ar Mista Kenyatta, wanda aka zaba a watan Maris.

Mista Kenyatta ya musanta tuhumce-tuhumcen, wadanda suka samo asali daga zarge-zargen cewa ya hura wutar rikicin da ya biyo bayan zabukan 2007 wadanda aka yi ta takaddama a kansu.

Masharhanta dai sun ce tuhumce-tuhumcen sun kara tagomashin yakin neman zaben Mista Kenyatta a zabukan bana, saboda masu kada kuri'a da dama na ganin shari'ar shisshigi ce a harkokin cikin gidan Kenya.

Karin bayani