Shugaba Issoufou ya kai ziyara Agades

Wani soja a barikin Agades
Image caption Wani soja a barikin Agades

Shugaba Muhammadou Issoufou na Nijar ya kara nanata cewa 'yan kunar bakin waken da suka kai hare-hare a garuruwan Agades da Arlit sun shiga kasar ne daga kudancin Libya.

Shugaba Issoufou ya furta hakan ne ranar Litinin, lokacin da ya kai ziyara barikin soja na Agades, inda 'yan kunar bakin waken suka kashe sojoji kimanin ashirin da hudu a harin na ranar Alhamis.

Shugaban kasar ta Nijar, wanda Kakakin Majalisar Dokoki Hamma Amadou da jagoran 'yan adawa Seyni Oumarou ke mara masa baya, ya ce akwai bukatar tsaurara matakan tsaro, a yunkurin dakile barazanar 'yan ta'adda.

Daga karshe ya ziyarci wuraren da aka kai hare-haren, ya kuma je ya yi ta'aziyya ga iyalan sojojin da aka kashe a hare-haren.

Baya ga Agades, an kuma kai hari a mahakar ma'adanin uranium ta SUMAIR dake Arlit, inda aka jikkata wadansu mutane.

Karin bayani