Shirin bunkasa tattalin arzikin Palasdinu

John Kerry
Image caption John Kerry na fatan bangarorin biyu za su koma kan teburin sulhu

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya kaddamar da wani shiri na dala biliyan hudu domin bunakasa tattalin arzikin Palasdinawa ta hanyar jawo hankalin masu zuba jari.

Da yake magana a wurin taron tattalin arziki na duniya a kasar Jordan, Mr Kerry ya ce shirin zai bunkasa tattalin arzikin Palasdinu da kashi 50 cikin dari a shekaru uku masu zuwa.

Shirin zai rage adadin marasa aikin yi ta hanyar gine-gine da kuma yawon bude ido.

Shugaban Isra'ila Shimon Peres ya yi kira ga Isara'ilar da Palasdinawa su koma tattaunawa domin kafa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta.

Aikin gina sabbin gidaje

Sanata John Kerry, wanda ke ziyara karo na hudu a yankin tun bayan hawansa kan wannan mukami a watan Fabrerun da ya gabata, ya ce shirin zai dogare ne kan ci gaban da aka samu a yunkurin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Mr Kerry tare da tsohon Fira Ministan Burtaniya Tony Blair, sun ce suna aiki tare da manyan 'yan kasuwa domin bunkasa tattalin arzikin Plasdinawan.

Aikin gina sabbin gidaje, da yawon bude da aikin noma, su ne bangarorin da za a mayar da hankali a kansu. Kuma fatan shi ne na rage yawan marasa aikin yi daga kashi 21 cikin dari zuwa kashi 8.

Masu sharhi dai na ganin matukar ba a fito fili an takawa Isra'ila birki ba, tare da kubutar da Palasdinawan daga mammayar da ta yi musu - ta hanyar basu 'yancinsu kamar kowacce kasa a duniya, to ba wani tsari na bunkasa tattalin arzikinsu da zai yi tasiri.

Karin bayani