Kawunan Tarayyar Turai ya rabu kan Syria

Ministocin harkokin wajan Tarayyar Turai
Image caption Ministocin harkokin wajan Tarayyar Turai

Ministocin harkokin waje na Tarayyar Turai na ganawa a Brussels domin tattaunawa a kan ko za a sassauta dokar hana shigar da makamai Syria, a kuma bari a kaiwa 'yan tawayen kasar makamai.

Burtaniya da Faransa na son a sauya dokokin ta yadda za su iya turawa 'yan tawayen da suka kira na tsaka-tsaki makamai.

Sakataran Harkokin Wajen Burtaniya, William Hague, ya ce yiwa dokar gyara zai sa Shugaba Assad ya tattauna a kan yadda za a kawo karshen rikicin ta hanyar siyasa.

Sai dai kuma kasashen Tarayyar Turai da dama ba su amince da wannan mataki ba—kasar Austria ta ce baiwa 'yan adawar Syria makamai zai yi zagon kasa ga yunkurin samar da zaman lafiyar da ake yi.

Karin bayani