An cire takunkumin makamai kan 'yan tawayen Syria

Ministocin harkokin wajan Tarayyar Turai
Image caption Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague ya yi maraba da matakin

Ministocin harkokin waje na Tarayyar Turai sun amince da kawo karshen takunkumin samar da makamai da suka kakaba a kan 'yan adawar kasar Syria.

Sai dai 'ba a dauki wani mataki nan take ba' kan baiwa 'yan tawaye na Syria makai, sannan sauran takunkumin za su ci gaba da aiki, a cewar sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague.

Matakin ya zo ne bayan doguwar tattaunawar da suka gudanar a birnin Brussels.

Matakai daban-daban na muzgunawa da aka kakaba wa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad za su kare ne a ranar 1 ga watan Juni.

Burtaniya da Faransa sun dade suna matsa lamba kan ganin an bayar da gudummawar makamai ga wadanda suka kira 'yan adawa masu matsakaicin ra'ayi a kasar ta Syria.

Suna masu cewa hakan zai taimaka a samu mafitar siyasa a rikicin da aka shafe shekaru biyu ana yi.

Mr Hague ya yi maraba da matakin da aka dauka a tattaunawar ta Brussels, yana mai cewa abu ne mai muhimmanci Turai ta nuna wa gwamnatin Assad cewa za a iya daukar kowanne mataki a kanta idan taki yarda a tattauna.

Karin bayani