Faransa ta goyi bayan Nijar a yaki da ta'addanci

Laurent Fabius
Image caption Laurent Fabius

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya ce Faransar za ta cigaba da kawo wa Nijar goyon bayanta a yakin da take yi da ta'addanci, da kuma kokarin da take na bunkasa tattalin arzikinta.

Mr Fabius ya kuma yi kira ga kasashen Afrika da su hada kai wajen yaki da barazanar da ke karuwa daga masu tsattsauran ra'ayin Islama a kudancin Libya.

Ya bayyana hakan ne bayan wata gaanawa da shugaban Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou a birnin Yamai.

Ziyarar ta Mr Fabius dai a kasar ta Nijar ta zo ne 'yan kwanaki bayan hare-haren kunar bakin wake 2 da aka kai a lokaci guda a wani barikin soja da ke birnin Agades, da kuma kamfanin hakar Uranium na Somair dake garin Arlit.

Sojan Nijar 24 ne suka hallaka a harin na ranar Alhamis da ta gabata.

Karin bayani