Pakistan: An kashe ma'aikatan riga kafi

Image caption Bara ma an kaiwa ma'aikatan Polio gari

An sake kaiwa ma'aikatan kiwon lafiya a Pakistan, hari yayinda suke ƙoƙarin yiwa yara allurar riga kafin cutar shan Inna ko Polio a garin Pashewar.

An kashe mace guda, yayin da wata kuma ta samu munanan raunika.

Yanzu dai ma'aikatan kiwon lafiya goma sha takwas ne da 'yan sanda uku dake ba su kariya, aka kashe a ciki ƙasa da shekara guda a ƙasar ta Pakistan.

An kuma an ɗora alhakin galibin hare-haren ne a kan 'yan ƙungiyar Taliban dake ƙasar ta Pakistan.