Burtaniya ta ce za ta iya fara baiwa 'yan adawan Syria makamai

William Hague
Image caption William Hague

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Hague ya ce gwamnatinsa za ta iya fara baiwa 'yan tawayen Syria makamai, tun daga yanzu, amma dai ya ce ba ta shirya yin haka ba tukuna.

Kalamansa na zuwa ne sa'o'i bayan da Burtaniya ta matsawa kungiyar Tarayyar Turai lamba a kan dage takunkumin haramta baiwa 'yan adawar Syria makamai.

Rasha dai wadda ita ce babbar kawar gwamnatin Syria, ta ce matakin turawa 'yan adawa makamai zai kara maida hannun agogo baya ne kawai.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rashar, Sergie Ryabkov ya ce matakin, wani abun takaici ne saboda ba zai yiwu ba a waje daya ka ce ka na son kawo karshen zubar da jini, sannan a daya hannun kuma ka tura karin makamai zuwa Syria.

Karin bayani