Uganda: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

Image caption 'Yan sanfa a ofishin jaridar Monitor

'Yan sanda kasar Uganda sun yi amfani da barkonon tsuhuwa wajen tawarwatsa masu zanga-zanga a harabar ofishin Jaridar Daily Monitor ta ƙasar.

Wakilin BBC a birnin Kampala ya ce an damƙe 'yan jarida biyu a yayin da aka lakaɗawa wasu da dama duka.

Tunda farko 'yan jarida da kungiyoyin fararen hula sun taru suna zanga-zanga a kan yadda 'yan sanda ke cigaba da rufe kamfanin jaridar tun a makon daya gabata.

Matakin 'yan sandan ya biyo bayan wata wasiƙa da jaridar ta Daily Monitor ta wallafa da wani Janar na soja ya rubuta a kan cewar Shugaba Yaweri Museveni na ƙoƙarin yadda ɗansa zai gajeshii, kuma duk wanda yayi adawa da hakan zai iya fuskantar kisa.