''Sojojin Burtaniya na tsare mutane ba bisa ka'ida ba''

Image caption Gwamnatin Burtaniya ta ce ya halasta da aka tsare 'yan kasar ta Afghanistan

An zargi sojojin Burtaniya da tsare mutane tamanin da biyar 'yan asalin kasar Afghanistan a wani haramtaccen sansani da ke Bastion a yankin Helmand.

Lauyoyin takwas daga cikin wadanda ake tsare da su sun ce ana tsare da wadanda suke karewa fiye da watanni goma sha hudu a sansanin da sojoji ke amfani da shi.

Sun bukaci babbar kotun da ke birnin London da ta bayyana mu su ko tsaron da ake yi wa mutanen na kan ka'ida.

Ma'aikatar tsaron Burtaniya ta ce ci gaba da tsare mutanen da ake yi ya halatta a karkashin dokokin Majalisar Dinkin Duniya.

Ta kara da cewa ana tsare da wadansu ne bisa zargi da hannu a kisan sojin Burtaniya ko kai hare-haren bom.

Karin bayani