Ana ranar dimokaradiyya a Najeriya

Image caption 'Yan Najeriya na ganin ba a samu ci gaba a-zo-a-gani ba

A Najeriya yau a duk faɗin ƙasar ana hutu domin cika shekaru goma sha huɗu da dawowa mulkin dimokaradiyya sai dai 'yan kasar da dama na ƙorafi dangane da yadda al'amura ke tafiya.

Duk da yake an kwashe wannan tsawon lokaci, 'yan kasar da dama na korafin kan rashin ci gaban da kasar ke fuskanta ta fannoni da dama.

Wani batu da ke ci gaba da jan hankalin mutane shi ne yadda yawanci ake zargin gudanar da magudin zabe a kasar.

Jami'yun adawa dai na zargin jam'iya mai mulki da hada baki da hukumar zabe wajen yin magudi, kodayake su ma ana zargin su da cewa duk kanwar ja ce.

Hukumar zaben kasar dai ta amince cewa 'yan siyasa na hada baki da wasu jami'anta wajen yin magudi, duk da yake ta ce tana hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan kunbiya-kunbiya.

Wasu 'yan siyasa sun shaidawa BBC cewa sai an sauya tsarin zaben kasar kafin a samu ingantar mulkin dimokaradiyya.

Karin bayani