Libya ta kori 'yan ƙasashen Afirka 1500

Image caption Yayin rikicin Libya baƙaƙen fata zun yi zargin an ci zarafinsu

A jamhuriyar Nijar wasu 'yan ƙasashen Afrika ta yamma kimanin dubu ƙaya da ɗari biyar sun isa Agades daga Libya tun ranar lahadin da ta gabata bayan korar da hukumomin Libya suka yi musu.

Mutanen suna dai zargin cewa hukumomin kasar Libiya ne suka umurce su da su fice daga kasar bayan an gana musu azaba iri iri a gidajen kason da aka tsare su.

Ya zuwa yanzu dai suna samun tallafi ne daga wasu ƙungiyoyin agaji irin su Red Cross a Agades ɗin kafin su samu wucewa zuwa ƙasashensu na asali.

Wasu 'yan Najeriya daga cikinsu sun koka da cewa, yanzu haka suna cikin wani hali saboda rashin kuɗin mota zuwa gida daga Nijar.