Amurka ta nemi Hezbollah da ta janye daga Syria

John Kerry, Sakataren Harkokin wajen Amurka
Image caption John Kerry, Sakataren Harkokin wajen Amurka

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci kungiyar 'yan Shi'a ta Lebanon, wato Hezbollah, ta janye mayakanta ba tare da bata lokaci ba, daga Syria.

Kakakin ma'aikatar Jen Psaki ta ce kasancewarsu a cikin Syria, abu ne mai hadari da ba za a amince da shi ba.

Hezbollah na taimakon gwamnatin Syria wajen kaddamar da hare-hare a garin kan iyaka na Qusair, inda aka rutsa da dubban fararen hula.

Tun farko dai, kwamitin kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniya ya yi Allawadai da amfani da mayaka 'yan kasashen waje a Qusair, a wani kuduri da Amurka ta gabatar.

Kasar Rasha, wadda ba ta da kuri'a a wannan kwamitin, ta ce matakin na son zuciya ne, kuma zai iya kawo tsaiko a tattaunawar samar da zaman lafiya a Syria.

Karin bayani