An kama kwarori da makamai a Kano

A Najeriya hukumomin tsaro sun ce sun gano wani gida a unguwar Bompai dake Kano inda aka jibge makamai.

Jami'an tsaron sun ce sun kuma cafke wasu mutane ukku, 'yan kasar Lebanon, dangane da wannan lamari.

Brigadier General Ilyasu Isa Abba ya ce, makaman sun hada da bindigogin atilare da bindigogin AK47 da nakiyoyi da albarusai.

Kamar yadda jami'in tsaron ya bayyana, kungiyar Hezbollah ce ta shigo da makaman a Najeriya, da zummar kai hari a kan duk wani abun da ke da alaka da Isra'ila da Amirka da kuma sauran kasashen yamma.

Tun shekara ta 2009 ake fuskantar hare-hare a wasu jihohin arewacin Najeriyar daga masu kaifin kishin Islama na kungiyar Boko Haram.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren.