Mali: Anyi zanga-zangar nuna adawa da Faransa

Image caption Mali tana ɗasawa da Faransa

Wasu mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna ƙyamar Faransa a garin Gao dake Arewacin Mali, suna masu zargin cewa, an ware su daga tattaunawar zaman lafiya.

Kuma masu zanga-zangar sun yi zargin cewa, Faransa tana goyon bayan ƙungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta MNLA.

A cikin watan Yuli ne dai aka shirya za'a gudanar da zabubuka a kasar ta Mali.

A farkon wannan shekarar ce dai Faransar ta tura sojojinta zuwa Malin domin katse hanzarin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai dake da alaka da kungiyar Al Qaida, waɗanda suka ƙwace iko da Arewacin kasar.