Maharin Woolwich ya bayyana a kotu

Daya daga cikin mutanen da ake tuhuma da kai hari a Woolwich
Image caption Mutumin da ake tuhuma da kashe wani soja a London ya bayyana a gaban kotu

Mutumin da ake tuhuma da kashe wani soja, Lee Rigby, a unguwar Woolwich da ke kudu maso gabashin birnin London ya bayyana a gaban kotu.

Michael Adebowale, mai shekaru 22, bai ce komai ba banda tabbatar da sunansa da adireshinsa a yayin dan gajeren zaman Kotun Majistare ta Westminster.

An ci gaba da tsare shi, sai kuma ranar Litinin mai zuwa zai sake bayyana a gaban Babbar Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Ingila da Wales, wadda aka fi sani da suna Old Bailey.

An tuhume shi ne bayan ya kwashe kwanaki shida a asibiti saboda harbinsa da 'yan sanda suka yi bayan harin na ranar 22 ga watan Mayu.

Har yanzu mutum na biyu da ake zargi, Michael Adebolajo, yana asibiti a karkashin kulawar 'yan sanda.

Shi ma Mista Adebolajo mai shekaru 28, 'yan sanda ne suka harbe shi a lokacin da aka kama shi.

Mista Adebowale, wanda kuma ake tuhuma da laifin mallakar makami, ya bayyana a kotun hannunsa daure da bandeji, 'yan sanda na kewaye da shi.

Yayin da ya nufi wurin da zai tsaya, an ga yana dingishi, kuma ya makale hannunsa na dama a jikinsa.

An dai dauki hoton mutanen biyu bayan harin, wanda suka kai da rana tsaka a wani titi mai yawan hada-hada.

Zuwa yanzu, 'yan sanda sun kama wadansu mutanen takwas a binciken da suke yi; amma an yi belin shida daga cikinsu yayin da aka saki biyu ba tare da wata tuhuma ba.

Karin bayani