Sojojin Najeriya sun saki mata da yara 58

Image caption Shugaban rundunar sojin Najeriya,Janar Ihejirika

Dakarun sojin Najeriya sun saki mata da kananan yara hamsin da takwas wadanda ake zargin su da alaka da yan Kungiyar Boko Haram.

Sojojin sun ce sun mika mata da kananan yara talatin da takwas zuwa ga gwamnan Jihar Yobe.

Haka kuma sun mika mata shida kananan yara goma sha hudu ga takwaransa na Borno.

Shugaban kasar Najeriya Good Luck Jonathan ya umarci a saki mata da kananan yara da ake tsare da su wadanda ake zargin na da alaka da yan Kungiyar.

Sai dai sakin mata da kananan yaran da ake zargin na da alaka da yan Kungiyar Ahlusunna lil dawai wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram na zuwa ne a lokacin da ake artabu tsakanin sojojin Najeriya da kuma 'yan Kungiyar musamman a Jihar Borno inda yan Kungiyar suka fi karfi.

Shugaban Kungiyar Imam Abubakar Shekau, ya sha nanata cewa an kame musu mata da kananan yara, ko a wani sakon video da ya fitar kwanakin baya; ya ce sun kama mata da yara saboda an kama matayen su da yaran su.

Kwamitin yin afuwa ga yan Kungiyar Boko haram da kuma yin sulhu na fatan wannan salon zai taimaka wajan aiwatar da sulhun tare da samun sa'ida kan halin tabarabarewar tsaro da ake ciki musamman a arewacin kasar.

Sai dai a wata sabuwar kuma dakarun sojin kasar sun bada sanarwar kame mutane hamsin da shida da ake zargin 'yan Kungiyar Ahlul sunna lil dawati wal Jihad ne; a ci gaba da artabun da ake yi a arewa maso gabacin kasar

Karin bayani