Majalisa ta dage zabuka a kasar Lebanon

Michel Suleiman
Image caption Shugaba Michel Suleiman na Lebanon

Majalisar dokokin Lebanon ta kada kuri'ar dage zaben da aka shirya yi watan gobe saboda damuwar da ake da ita a kan yiwuwar bazuwar rikicin da ake fama da shi a Syria zuwa cikin kasar.

'Yan majalisar sun amince su tsawaita wa'adinsu da watanni 17-- wanda shi ne karon farko da akayi hakan tun da aka kawo karshen yakin basasar kasar a shekarar 1990.

Wata hujjar da ta sa aka dage zaben kuma itace gazawar 'yan majalisar su amince da sabuwar dokar zabe.

Wadanda ke goyan bayan dage zaban, sun ce hakan zai iya rage fargabar da ake da ita, wadda ta karu bayan shigar kungiyar Hezbollah yakin da ake yi a Syria inda suke fada a bangaren gwamnati.

Karin bayani