Mayakan Islama na Libya sun shiga yakin Syria

Image caption Masu kishin Islama a Libya sun shiga Syria

Wani jagoran mayaka a kasar Libya ya gaya ma BBC cewa mayaka 'yan kishin Islama, wadanda suka taimaka aka hambarar da Kanar Gaddafi, sun shiga yakin da ake gwabzawa a kasar Syria.

Salem el Derby, wanda ya kafa Abu Salim Brigade a Derna, babban yankin da masu kaifin kishin Islama suka fi yawa a kusa da Benghazi ya ce, danniyar da gwamnatin Gaddafi ta rinka nunawa masu akidojin Musulunci ta sanya wasu masu adawa da ita, rungumar akidoji masu tsauri na Islama.

Ya ce da yawa daga cikin su sun fada gwagwarmaya a wasu kasashe; don haka ake kashe 'yan kasar ta Libya da dama a kulli-yaumin a Syria, a fadan da suke yi a bangaren 'yan tawaye.

Karin bayani