Jamhuriyyar Nijar na fadakarwa kan tsaro

Image caption Nijer na fadakar da alumma kan tsaro

Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani shirin fadakar da jama'a, ta yadda za su ba da goyon baya da hadin kan da ya dace don tabbatar da tsaro a cikin kasar.

Matakin na daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka don karfafa tsaro sakamakon hare-haren da wasu 'yan kunar-bakin wake suka kai a barikin sojan Agadez da kamfanin hakar Uranium na Somair da ke Arlit a makon da ya gabata.

Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar sojojin gwamnati ashirin da hudu da maharan su bakwai.

Karin bayani