ICC ta yi watsi da bukatar Libya a kan SaifulIslam

Image caption Saif Gaddafi

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC ta yi watsi da bukatar kasar Libya kan batun shari'ar Saif Gaddafi.

Kotun kuma ta tunatar da Libya a kan ta cika alkawarinta na mika dan tsohon shugaban Libya, Kanar Gaddafi don kotun tayi masa shari'a.

Kotun ICC da gwamnatin Libya duk suna tuhumar Saif Gaddafi da aikata laifuka lokacin juyin juya hali a kasar a shekara ta 2011.

A baya dai, Saif Gaddafi ya bayyana gaban wata kotu a Zintan dake kudancin Libya, wanda ke kusada inda mayakan suka damke shi a watan Nuwambar 2011.

Karin bayani