Kotu ta tilasta gudanar da zabe a Zimbabwe

Image caption Abokan hamayya Mugabe da Tsvangirai

Kotun kolin kasar Zimbabwe ta ce dole ne a gudanar da zaben shugaban kasa dana 'yan majalisar dokoki daga nan zuwa ranar 31 ga watan Yuli.

Kotun tsarin mulkin ta bukaci Shugaba Robert Mugabe ya saka ranar zabukan ba tare da bata lokaci ba.

Mista Mugabe na jam'iyyar Zanu-PF da alamu zai kara da shugaban jam'iyyar MDC, Morgan Tsvangirai a zaben shugaban kasa.

Mista Tsvangirai ya kasance Pirayi Minista a gwamnatin Mista Mugabe ta hadin gwiwa da aka kafa bayan takaddamar data biyo bayan zaben shekara ta 2008.

A makon daya gabata aka sanya hannu a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Tun a shekarar 1980, Mista Mugabe ke jan ragamar kasar ta Zimbabwe.

Karin bayani