Qardawi ya yi kira ga 'yan Sunni da su shiga yakin Syria

Sheikh Yusuf al-Qardawi
Image caption Sheikh Yusuf al-Qardawi

Fada na ci gaba a kokarin kwace iko da garin al-Qusair a yammacin kasar Syria, inda dakarun gwamnati , da mayakan kungiyar Hizbullah ta Yan shi'a a Lebanon, suka yi ma 'yan tawaye kofar-rago.

A waje daya, wani fitacen malami na 'yan Sunni ya yi kira ga yan Sunni a yankin da su je Syria domin kai dauki wajen yaki da gwamnatin kasar.

Sheikh Yusuf al Qardawi ya fada ma wani gangami a Qatar cewa dukkan wani dan Sunni dake da sauran karfin zuwa fagen -daga ya kama ta ya je Syria domin shiga cikin dakarun 'yan tawayen.

Rahotannin dak efitowa daga al Qusair na cewa mutane na cikin wani mawuyacin hali, musamman fararen hular da aka raunata kuma suka kasa ficewa a sakamakon fadan.

Akwai fararen hular da ake cewa an kashe yayinda suka yi kokarin tserewa.

Akwai rahotannin cewa an kashe wasu iyali guda su bakwai da suka yi kokarin gudu daga garin Dabaa, arewa da garin na al-Qusair.