Kotu a Masar ta ce zaben majalisar dattawa ba ya kan ka'ida

Majalisar Dattawan Masar
Image caption Majalisar Dattawan Masar

Kotun kolin Masar ta yanke hukuncin cewa, an zabi majalisar dattawan kasar ne ta hanyar da ta sabawa doka.

Kotun ta bukaci a rushe majalisar ta Shura da zarar an zabi sabbin 'yan majalisa.

Sai dai kuma har yanzu ba a sanya lokacin yin zaben 'yan majalisar dokokin ba.

Wasu masana shari'a a Masar na cewa hukuncin ba zai yi wani tasiri ba, domin kuwa majalisar zata ci gaba da kafa dokoki har sai an kafa sabuwar majalisar dokoki.

Wannan hukunci ya kara dagula al'amurra a tsarin shari'ar kasar ta Masar , inda lauyoyin 'yan adawa da masu goyon bayan gwamnati ke kalubalantar ingancin dokokin da ake aiki da su a tsarin shugabancin kasar.