Qusair: Fararen hula suna cikin wani hali

Image caption Ana fama da ƙarancin abinci a garin Qusair

Jami'an diplomasiyya a Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwa game da halin da ake ciki a birnin Qusair, kuma kungiyar agaji ta Red Cross tace fararen hula suna cikin wani hali a garin.

Lamarin abin damuwa ne musamman yadda ya shafi farar hula.

Sojojin gwamnati na cigaba da kai hari a birnin dake hannun 'yan tawayen fiye da makonni biyu da suka wuce, an kuma rutsa da mazauna birnin wadanda ke fuskantar karancin abinci da ruwan sha da magunguna.

To amma jami'an diplomasiyyar sun ce Rashar ba za ta goyi bayan shelar ba saboda Majalisar Dinkin Duniyar ba ta yi komai ba a kan batun lokacin da 'yan tawaye suka mamaye birnin.

A ranar Asabar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar agaji ta Red Cross a lokaci guda sun nemi a bayar da kofar shiga cikin birnin na Qusair da gaggawa.

Karin bayani