Masu zanga-zanga sun yi artabu da 'yan sanda

zanga zanga a Turkiyya
Image caption Masu zanga-zangar sun yi kira ga Erdogan ya yi murabus

Masu zanga-zanga a Turkiyya sun sake yin artabu da 'yan sanda a kan titunan birnin Santanbul a daren ranar Lahadi.

Mahukutan kasar sun sake yin amfani da mesar ruwa da barkonon tsohuwa domin tawartsa masu zanga-zangar, wadanda suka taru a filin wasan kwallon kafa na Besitkas, a yanayi mafi muni tun bayan barkewar tarzomar.

An rika yin amfani da masallatai a matsayin asibitoci na wucin gadi domin bai wa mutanen da suka ji raunuka magunguna.

Yayin da ake ci gaba da zanga zangar nuna adawa da gwamnati a Turkiyya, Praministan kasar, Recep Tayyip Erdogan, ya sake yin tur da masu zanga-zangar, yana mai bayyana su da cewar makiya dimokradiyya ne.

Mista Erdogan ya yi watsi da sukar da ake yi masa cewa gwamnatinsa na yin kama-karya, kuma tana tsaurara ra'ayin Islama, yana mai cewa a karkashin jagorancin jam'iyyarsa tattalin arzikin kasar ya habaka.

Ya ce wadanda ke zanga-zangar kungiyoyi ne 'yan tsiraru wadanda wasu daga wajen kasar ke marawa baya suna kafa hujjoji marasa tushe.