Woolwich:Adebolajo ya bayyana gaban kotu

Image caption Micheal Adebolajo da Micheal Adebowale a kan titin Woolwich a London

Mutane biyun da ake zargi da kashe wani sojin Birtaniya a nan London cikin watan da ya wuce sun yi wata 'yar gajeruwar bayyana a gaban kotu.

Michael Adebolajo mai shekaru 28 ya bayyana a karon farko tun lokacin da 'yan sanda suka tuhume shi a ranar asabar, kuma an ci gaba da tsare shi.

Michael Adebolajon, wanda ya kwashe kwana tara kwance a asibiti, ya je kotun ne, hannunsa na hagu daure a bandeji, kuma yana sanye da karamar riga fara da kuma Alkur'ani a hannunsa.

An gayawa kotun cewa, yana son a rika kiransa: Mujaheed Abu Hamza.

Lauyansa, DAvid Gottlieb, ya ce, ba zasu nemi a bada belinsa ba.

Shi kuma daya wanda ake zargin abokin yinsa ne, Michael Adebowale, dan shekaru ashirin da biyu, a makon da ya wuce ne ya bayyana a gaban kotun majistare, inda aka tuhume shi da aikata kisan kai, da kuma mallakar bindiga.

Masu gudanar da bincike a kan kisan sojan, Lee Rigby, sun kuma kama wasu mutanen goma, an zargi takwas daga cikinsu da hada baki wajen aikata kisa; biyun kuma an caje su da samar da bindigogi ba bisa ka'ida ba.

An saki biyu daga cikin mutanen goma ba tare da wata tuhuma ba, yayin da ake cigaba da tsare sauran takwas.

Karin bayani