Japan zata iya baiwa Ghana bashi

Image caption John Mahama, shugaban kasar Ghana

Gwamnatin Japan ta ce za ta koma baiwa ƙasar Ghana bashin kuɗaɗe, a cikin wani shirin gudunmuwa ga ƙasar ta Ghana, da ƙasar Japan din ta dakatar a shekara ta 2001.

Japan dai ta dakatar da bashin ne saboda ƙasar ta Ghana ta shiga rukunin ƙasashen da bashi ya yiwa kanta.

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama ne ya bayyana haka a taro kan raya ƙasashen Afrika da aka kamalla yau a birnin Yokohama na ƙasar Japan.

Yanzu dai Japan ta yi alkawarin zuba jari da bada tallafi da ya kai na dalar Amurka biliyan talatin da biyu a kasashen Afurka