An bukaci masu zanga-zanga su maida wukar

Turkiyya zanga-zanga
Image caption Masu zanga-zangar sun nemi Fryministan kasar ya ajiye mukaminsa

Mataimakin Pirayi Ministan Turkiyya, Bulent Arinc, ya nemi afuwar masu rajin kare muhalli wadanda kokarin da suke na kare wajen shakatawa na birnin Santanbul, ya rikide zuwa zanga-zangar kyamar gwamnatin da ba'a taba ganin rinta ba a kasar.

Mr Arinc ya yadda kan cewa amfani da barkon tsohuwa da 'yan sanda su ka yi ne, ya kara rura wutar zanga-zangar kan abin da ya kira korafe-korafen da basu saba doka ba.

Ya kuma yi kiran a kawo karshen zanga-zangar ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa wasu da ya kira 'yan ta'adda sun shiga cikinta.

Daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago na kasar sun fara yajin aikin kwanaki biyu kan goyan bayan zanga zangar.