CAN ta nemi a kama Buhari

Nigeria can and Buhari
Image caption Janarar Muhamadu buhari ya zargi gwamnati Najeriya da nuna rashin adalci

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato CAN, ta bukaci Shugaban kasar da ya ba da umurnin a tsare dan takarar Jam'iyyar adawa ta CPC a zaben shekarar 2011, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, saboda kalaman da kungiyar ta yi zargin cewa ya furta wadanda a cewarta babbar barazana ce ga wanzuwar Najeriyar a matsayinta na kasa.

Kungiyar ta CAN dai ta yi zargin cewa, a wata hira da ya yi da wani gidan rediyo mai zaman kansa a Kaduna a karshen mako, tsohon shugaban kasar ya zargi Shugaba Goodluck Jonathan da nuna bambaci a yadda yake tunkurar matsalar 'yan Kungiyar Boko Haram da kuma yadda gwamnati ta tunkari matsalar masu ta da kayar baya a yankin Neja Delta.

Ta ce kalaman na Janarar Buhari sun tayar mata hankali saboda a ganinta bai kamata ya kare 'yan kungiyar Boko haram ba a matsayinsa na tsohon shugaban kasa.

Sai dai wani na hannun daman Janar Muhammadu Buhari wanda kuma shi ne dan takarar Gwamna na jam'iYyar CPC a jihar Jigawa a zaben sherkarar 2011, Hon Faruk Adamu Aliyu, ya yi watsi da zargin ta kungiyar kiristocin Najeriyar ta yi