Dubban mutane sun bar gidajensu a Czech

Ambaliyar ruwa
Image caption Amnaliyar ruwa a Turai

Dubban mutane sun bar gidajensu a Jamhuriyar Czech, inda ruwan koguna ke barazanar tumbatsa ya shallake shingayen da aka kakkafa don hana ambaliya bayan an kwashe kwanaki ana sheka ruwan sama.

Tuni dai ruwan ya mamaye wasu daga cikin garuruwan kasar ta Czech; kuma an yi gargadin cewa a cikin sa'o'i kalilan ruwan zai iya shallake shingayen.

Ruwan dai yana gangarawa ne zuwa kasar Jamus, inda dubban sojoji ke taimakwa da aikin karfafa shingaye a biranen da ke kudanci da gabashin kasar.

Mutane akalla goma ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa wacce kuma afkawa kasashen Austria da Switzerland