An yi amfani da Sarin a Syria! Inji Faransa

Ministan harkokin wajan Faransa, Laurent Fabius
Image caption Ministan harkokin wajan Faransa, Laurent Fabius

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya ce akwai kwararan shaidun da ke nuna cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da sinadarin Sarin mai guba akan mayakan 'yan tawayen kasar.

Mr Fabius ya ce, gwaje-gwajen da aka yi a Faransa na jini da fitsarin mutanen da harin garin Sareqeb na watan Afrilu ya shafa, sun nuna alamun sinadarin Sarin din.

Ya ce yanzu haka an mika wa Majalisar Dinkin Duniya sakamakon gwaje-gwajen.

Amurka ta ce akwai bukatar a samu karin wasu shaidu kafin a bayyana cewa an yi amfani da sinadarin Sarin din a Syria.

Karin bayani