'Boko Haram da ANSARU 'yan ta'adda ne'

jonathan
Image caption Shugaba Jonathan na Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da wata doka da ta haramta kungiyar Jama'atu AhlusSunna Lida'awati wal jihad, da ake yiwa lakabi da Boko Haram da kuma kungiyar Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan wadda ake kira ANSARU, tare da bayyana kungiyoyin a matsayin masu aikin ta'addanci.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce, akwai hukunci mai tsauri ga duk wanda ya yi alaka da wadannan kungiyoyin.

Sanarwar ta ce duk wanda yayi mu'amala da kungiyoyin biyu zai fuskanci hukuncin daurin shekaru ashirin a gida yari.

A ranar Litinin ne gwamnatin Amurkan ta ce za ta bada tukwicin dala miliyan 23 da ga duk wanda ya taimaka wajen kama wasu shugabannin kungiyoyin 'yan ta'adda ciki hadda Abubakar Shekau na Boko Haram.

Karin bayani