Neman kawar da kyamatar masu Sida

A Najeriya, kwamiti mai kula da harkokin kiwon lafiya a majalisar dattawan kasar, ya yi zama don sauraron ra'ayoyin jama'a a kan masu fama da cutar AIDS ko SIDA.

Kwamitin yana duba yiwuwar yin dokar da za ta hana nuna wariya ga masu cutar AIDS tare da ba su magani kyauta.

Kungiyoyi da dama ne suka halarci zaman, ciki har da masu rajin kare hakkokin masu fama da cutar.

Ana kukan cewa kimanin kashi daya bisa uku ne kawai na wadanda aka san sun kamu da cutar ta AIDS suke samun magunguna.

A wajen zaman an bayyana cewa, adadin masu fama da SIDA zai kai miliyan biyar a kasar.