Kudurin dokar saukaka tsige Shugaban Najeriya

Image caption Ginin Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya, Majalisar wakilan kasar ta amince da karatu na biyu na wani kudurin doka, da zai saukaka matakan da za a bi wajen tsige shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa daga mukaminsa.

Kudurin dokar da aka tafka zazzafar mahawara akai kafin a amince da shi, zai baiwa 'yan majalisar wuka da nama a yunkurin tsige shugaban kasa, idan akwai dalilan yin hakan, ba tare da bi ta ofishin babban jojin kasar ba.

A cewar wani dan majalisa, Jerry Manwe daga jihar Taraba, kudurin dokar bawai rashin girmama matsayin ofishin Shugaban kasa ko na mataimakinsa bane.

Karin bayani