Amurka ta ce za ta yi taka-tsantsan wajen ba da tukwici

Nigeria Amurka
Image caption Jagoran kungiyar Boko Haram

Wasu kusoshin ma'aikatar harkokin wajen Amurka sun ce kasar za ta yi matukar taka-tsantsan wajen bayar da lada ga duk wanda ya taimaka aka kama shugabannin wasu kungiyoyin masu ta da kayar baya a yammaci da arewacin Afirka.

Gwamnatin kasar ta Amurka dai ta bayyana aniyar bayar da lada ne a karkashin wani shirinta na yaki da ta'addanci, ga duk wanda ya lalubo shugabannin kungiyoyin da ta ce na 'yan ta'adda ne.

Kasar ta Amurka ta ce za ta bayar da kudi har dala miliyan bakwai, ga duk wanda ya kawo bayanan da za su kai ga kama Imam Abubakar Shekau, wato jagoran kungiyar Jama'atu AhlisSunnah lid Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da suna Boko Haram; yayin da aka ware dala miliyan biyar ga wanda ya taimaka aka kama wasu shugabannin kungiyar AlQaeda a yankin Maghrib su biyu.

A jiya ne Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da wata doka da ta haramta kungiyar ta Boko Haram da kuma kungiyar Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan wadda ake kira Ansaru, tare da bayyana kungiyoyin a matsayin masu aikin ta'addanci.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce, akwai hukunci mai tsauri ga duk wanda ya yi alaka da wadannan kungiyoyin.

Sanarwar ta ce duk wanda ya yi mu'amala da kungiyoyin biyu zai fuskanci hukuncin daurin shekaru ashirin a gida yari.