Yunkurin kwace iko da Kidal

Rundunar sojan Mali ta ce ta kwace iko da kauyen Anefis na arewacin kasar, bayan mummunan fada da 'yan tawayen Azbinawa na MNLA.

Artabun ya biyo bayan sanarwar da sojoji suka bayar, cewa zasu yi yunkurin sake kwace iko da garin Kidal, wanda shi ne na karshe dake hannun 'yan tawayen, gabanin zaben da za a gudanar na shugaban kasa a karshen watan Yuli.

Wani mai magana da yawun 'yan tawayen ya shaidawa BBC cewa an kashe mayaka akalla biyu a fadan, an kuma raunata wasu.

Wannan ne karon farko da rundunar sojan Mali ta gwabza da Abzinawan masu neman ballewa, tun bayan tsoma bakin sojojin Faransa a rikicin a watan Janairu.

An koma tattaunawa a Burkina Faso tsakanin 'yan tawayen da gwamnatin wucin gadin Mali.

Wakilin BBC a Mali ya ce, babu tabbaci ko Faransa za ta kyale sojojin Mali su afkawa Kidal yayin da shawarwarin ke gudana.