Tamowa na kashe yara miliyan uku

Children malnutirtion
Image caption Kafar wani jinjiri dake fama da Tamowa

Sakamakon wani bincike da mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ta wallafa ranar Alhamis ya bayyana cewa tamowa ce ke yin ajalin kusan rabin daukacin yara 'yan kasa da shekaru biyar din da ke mutuwa a fadin duniya.

Rahoton ya ce fiye da yara miliyan uku ne ke tamowa ke sanadin mutuwarsu duk shekara, akasarinsu a Afirka da Asiya.

Wannan rahoto dai ya zo ne gabanin wani taron kasa-da-kasa da za a gudanar a karshen wannan makon a karkashin shugabancin Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron.

Kungiyoyin agaji sun yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da su samar da karin kudi dala biliyan daya a kowace shekara domin magance yawan mace- macen yara kanana.

Tamowar dai na hana girma da kuma ba su da kuzari sosai saboda rashin samun abinci mai gina jiki .

Haka kuma tana barazana ga rayuwar mata masu juna biyu.