Hukunci a kan rikicin jam'iyyar CDS-Rahama

Tutar Jumhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jumhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar kotun kolin kasar ta ba Alhaji Abdou Labo, gaskiya a rikicin da yake yi da shugaban jam'iyyar CDS- Rahama, Alhaji Mahaman Ousmane .

Hukuncin, wanda shi ne na karshe a shari'ar da bangarorin biyu ke yi tun 2011, ya soke babban taron Congres da jam'iyyar ta yi a 2011 a Damagaram da duk wasu matakan da ya dauka.

Hakan dai yana nufin matakin korar da taron na Congres ya yi wa Alhaji Abdou Labon da wasu mukarabansa daga jam'iyar ba sa kan ka'ida.

Ga dukkan alamu a yanzu wajibi ne jam'iyar ta sake shirya wani taron Congres da zai zabi sabbin mambobin kwamitin gudanarwa.

Rikici tsakanin bangarorin biyu dai ya taso ne lokacin zabubukan 2011 inda bangaren abdu labon ya zabi mara ma dan takaran jam'iyar PNDS-Tarayya, Alhaji Mahamadou Issoufou, baya yayinda bangaren Alhaji Mahaman Ousmane ya bi Alhaji Seyni Omar na MNSD- Nasara