PDP a Sokoto ta ce ba a yiwa gwamna adalci ba

PDP
Image caption Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya

Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Sokoto ta ce ba a yiwa gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko adalci ba akan dakatar da shi da jam'iyyar ta kasa ta yi.

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriyar ta yi karin haske a kan dalilan da ya sanya ta dakatar da gwamnan.

Jam'iyyar ta ce ta yanke shawarar dakatar da gwamnan na Sokoto ne tun kafin a gudanar da zaben kungiyar Gwamnoni ta Najeriya da ya haifar da kace-nace.

Jam'iyyar ta ce a lokuta da dama shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya sha kokarin samun gwamnan amma hakan ba ta yiwu ba, kuma an gayyace shi taro a ranar biyar ga watan Yuni, gwamnan ya sa kafa ya fice daga Najeriyar.

A jiya ne dai kwamitin gudanarwar jam'iyyar PDP din na kasa ya bayar da sanarwar dakatar da gwamnan, bisa zargin cewa ya yi wadansu abubuwa na rashin da'a.

Sai dai wani na hannun damarsa kuma dan Majalisar Wakilan Najeriya, Hon Shu'aibu Gwanda Gobir, ya ce jam'iyyar ba ta kyauta wa gwamnan ba.

Haka kuma reshen jama'iyar PDP na jihar Sokoto ya mayar da martani dangane da dakatar da gwamnan, inda ya yi zargin cewa wasu ne da ke neman wargaza jam'iyyar PDPn ya sa suke daukar matakan dakatar da wasu 'ya'yan jam'iyyar da suka taimaka mata wajen samun nasara.

Alhaji Muhammadu Dangoggo,shugaban jam'iyar PDP na karamar hukumar Sokoto ta Arewa, ya ce Gwamna Wammako bai dakatu ba.

Gwamna Wamakko ne dai gwamna na biyu da jam'iyyar ta dakatar a 'yan kwanakin nan, bayan zaben da kungiyar gwamnonin kasar ta gudanar.

Masana dai na bayyana dambarwar da jam'iyyar ta PDP ke fama da ita da cewa take-taken wargajewarta ne, amma jam'iyyar ta musanta hakan.