Shugaba Putin na Rasha ya rabu da matarsa

Putin da Lyudmila
Image caption A 'yan shekarun nan da kyar ake ganin su tare

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, da matarsa Lyudmila sun sanar a gidan talabijin din kasar cewa, aurensu ya mutu.

Lyudmila ta ce, shawara ce ta bai daya suka dauka, tana mai cewa aiki ya dauki hankalin mijin na ta.

Ta ce 'ya'yansu sun girma, kowace ta kama gabanta, kuma ba ta son shiga idon jama'a da kuma zirga-zirga a jiragen sama.

An dai sha yin jita-jita a kafofin yada labarai dangane da dangantakar mutanen biyu, saboda a 'yan shekarun nan da kyar ka gan su tare.

Kusan shekaru talatin kenan da Vladimir Putin ya auri Lyudmila, kuma suna da 'ya'ya biyu mata.

Karin bayani