Erdogan ya ce ba gudu, ba ja da baya kan shirinsa

Recep Tayyip Erdogan, Pirayim Ministan Turkiya
Image caption Recep Tayyip Erdogan, Pirayim Ministan Turkiya

Pirayim ministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da shirinta na yin gini a wani wurin shakatawa da ke birnin Santambul, duk kuwa da zanga zangar da aka kwashe kwana da kwanaki ana yi, wadda a wasu lokutan ta munana.

Ya ce, masu tsatsauran ra'ayi ne ke tafiyar da masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Pirayim minista Erdogan na magana ne a Tunisia, bayan ya katse ziyarar da yake a arewacin Afirka, don komawa gida.

Bayan kalaman Pirayim ministan, daya daga cikin manyan kungiyoyi masu kamfen din, ta yi kira ga jama'a da su fito su yi zanga zanga yau da yamma, a duk fadin kasar.

An dai bayar da rahoton cewar mutane hudu sun mutu sannan wasu dubbai sun samu raunuka a tashin hankali kawo yanzu.

Karin bayani