Jami'an tsaro sun kammala ziyara a Borno

Image caption Sojoji sun ce ba a hana kai abinci garin Bama ba.

Jami'an rundunar sojan Najeriya sun kammala ziyarar gani da ido tare da manema labarai zuwa wasu sansanoni da sojin ke ikirarin cewa na 'yan kungiyar Boko Haram ne kafin su kore su a arewacin jihar Borno.

Wakilin BBC wanda ke cikin tawagar da suka ziyarci jihar ya ce kodayake ba a bar su sun tattauna da jama'a a Maiduguri ba, amma wani dan jarida da ke aiko da rahotanni daga yankin ya shaida masa cewa mazauna birnin na bayyana cewa sojoji suna gallaza mu su.

Dan jaridar ya ce jami'an tsaro na yin taka-tsantsan wajen gudanar da ayyukansu tun bayan da aka sanya dokar ta-baci.

Kazakila, BBC ta fahimci cewa mazauna garin Bama da kewayensa na korafin cewa ba a bari a shigar da kayayyakin abinci cikin garin.

Sai dai kakakin rundunar JTF, Laftanal Kanal Sagir Musa, ya musanta wannan zargi, yana mai cewa ana shigar da kayayyakin abinci garin idan hakan ta kama.

A cewarsa, '' ana sane da korafe-korafen da jama'a ke yi, inda kuma aka ga korafe-korafen sun tabbata gaskiya muna daukar mataki. Mun yi taro da mutanen Bama cewa duk lokacin da suke bukatar abinci za a kai musu.''

Karin bayani