An kaddamar da katafaren asusun neman gudumawa don Syria

Yangudun hijirar Syria
Image caption Yangudun hijirar Syria

Hukumomin agaji na majalisar dinkin duniya sun yi kira mafi karfi a tarihin majalisar, don samun kudaden gudanar da aikace aikacensu a kasar Syria da makwabtanta.

A yanzu suna neman karin dala biliyan hudu a wannan shekarar, baya ga dala biliyan daya din da suka bukata tun farko.

Majalisar ta yi hasashen cewa, yawan 'yan gudun hijira da kuma sauran masu bukatar taimako a cikin Syria, zai karu matuka: Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan agaji, Valerie Amos ta ce,"mun kiyasta cewa, a yanzu haka mutane miliyan shidda da dubu dari takwas ne ke bukatar taimakon gaggawa - watau kashi daya cikin uku na al'ummar Syria."

Karin bayani